Guidance

Notice of rights and entitlements Hausa (PACE Code H) (accessible version)

Updated 11 March 2019

Dokar hana aikata ta’addanci ta shekara ta 2000

KA TUNA ‘YANCINKA/KI A LOKACIN DA KAKE TSARE

A wadannan bayanan an tabbatar maka da ‘yancin ka a karkashin dokar Ingila da Yankin Wales, kuma yayi daidai da yarjeniyar dokokin kasashen Turai na shekarun 2012 zuwa 2013 akan ‘yancin bil’adama na ikon samun bayyanai a lokacin da ake gudanar da shari’ar da ta shafi aikata laifufuka

An takaitata bayanan ‘yancin da kake da a wannan shafi a ofishin ‘yan sanda

Kuma akwai Karin bayanai a sakin layi na daya zuwa goma sha daya a shafukan gaba

Kuma akwai cikkakun bayanai a tsarin dokokin ‘yansanda na H

  1. Ka gaya wa ‘yansanda in kana son taimakon Lauya a lokacin da kake cikin ofishin ‘yansanda. Ba sai ka biya kudi ba.
  2. Ka gayawa ‘yansanda idan kana son a gaya wa wani cewa kana ofishin ‘yansanda. Ba sai ka biya kudi ba.
  3. Ka gayawa ‘yansanda idan kana son ganin dokokin ‘yansanda – Ana kiransu tsarin dokokin da ‘yansanda ke amfani dasu
  4. Ka gayawa ‘yansanda idan kana son a yi maka magani Ka kuma gaya ma yan’sanda idan kana jin ciwo ko kuma ka samu rauni. Bada magani kyauta ne.
  5. Idan aka maka tambayoyi akan wani zargin da akeyi maka a sa hannu,ko shirya,ko haddasa aikin ta’addanci, to ba dole ba ne ka yi magana. Sai dai kuma, hakan zai iya yin illa ga kariyar da kake da idan ba ka ambaci abin da aka tambayeka ba wanda daga bisani za ka dogara da shi a kotu. Za a iya bayar da duk abin da ka fada a matsayin shaida.
  6. Dole ne yansandan su yi maka bayani a akan tuhumar da akeyi maka game da sa hannun ka ko shirya ko haddasa aikata ta’addanci. Kuma da dalilin da yasa aka kama ka aka kuma tsare ka
  7. Dole ne ‘yansanda su baka ko lauyanka damar ganin rubutattun bayanai da takardu game da dalilin kama ka da kuma tsare ka da aka yi da kuma lokacin da za ka ke a ofishin ‘yansanda.
  8. Dole ne ‘yansanda su samo maka tafinta, in kana bukata. Haka kuma za a iya fassara maka wasu takardun bayanai. Ba sai ka biya kudi ba.
  9. Gayawa ‘yansanda idan kai ba dan Birtaniya ba ne kuma idan kana son tuntubar ofishin jakadancin kasarku ko kuma kana son a gaya musu cewa kana tsare. Ba sai ka biya kudi ba.
  10. Dole ne ‘yansanda su gaya maka tsawon lokacin da za su iya tsare ka.
  11. Idan aka tuhume ka kuma shari’arka ta je kotu, kai ko lauyanka na da ‘yancin ganin shaidun da masu gabatar da kara kafin a fara sauraron karar a kotu

Ka gayawa jami’in yan’sanda idan baka fahimci bayanan da suka shafi ‘yancin ba

Ka duba shafuka na kan takaitattun bayanai domin samun bayanan yadda yan’sanda zasu kula da kai

Wannan Sigar Sanarwar Hakkoki da Da’ aowi ya fara aiki ne daga biyu ga watan daya na Disamba shekara na dubu buyu da sha takwas (2018)

Ka tabbatar ka ajiye wannan bayanai kuma ka karanta bada wani bada lokaci ba . Zasu taimakama, yanke shawara a lokacin da ka ke cikin ofishin yan sanda.

1. Samun lauya ya taimake ka

  • Lauya zai iya taimakon ka kuma ya bada shawara akan doka.
  • Neman magana da lauya bai nuna cewa ka aikata laifi ba.
  • Dole ne jami’in yan’sanda ya tambaye ka ko kana bukatar shawara ta fuskar doka.
  • Dole ne yan sanda su tabbatar sun baka damar yin magana da lauya a kowani lokaci kake bukata,dare ko rana a lokacin da kake ofishin yansanda.
  • Idan ka nemi shawara bisa doka, bai kamata yan’sanda su yi maka tambayoyi ba,har sai ka samu yin magana da lauya. Idan yan’sanda sun yi maka tambaya,zaka iya ce wa kana bukatar lauya a dakin.
  • Idan ka gayawa wa ‘yansanda cewa ba ka bukatar shawara ta fuskar doka, kuma daga bisani ka canja ra’ayinka, sai ka jami’in ‘ yan’sanda, wanda zai taimake ka wajen samun lauya.
  • Idan lauya bai zo ba,ko kuma bai tuntube ka ba a ofishin yan’sanda,ko kuma kana bukatar magana da lauya, sai ka gaya wa yan’sanda su sake tuntubar maka lauya.
  • Zaka iya neman yin magana da lauyan da ka sani kuma ba sai ka biya kudi ba idan suna aikin bada taimako ta fuskar sharia.Idan baka san wani lauya ba, ko kuma ba’a iya tuntubar lauyan da ka sani, zaka iya magana da lauyan dake aiki anan.Ba sai ka biya kudi ba.
  • Babu wata dangantaka tsakanin lauyan dake aiki anan da kuma ‘yan sanda.

Idan za’a shirya baka shawara ta fuskar shari’a ba tare da ka biya ba.:

  • ‘Yan sanda zasu tuntubi Cibiyar da ake neman lauya mai karewa (DSCC). Cibiyar DSCC za ta shirya lauya ya baka shawarar da ya cancanta, ko kuma daga lauya mai aiki a nan.
  • Ita Cibiyar da ake neman lauyan mai kariya(DSCC) mai zaman kanta ne dake da alhakin shirya bada whawara ta fuskar ba tare da biyan kudi ba sannan kuma bata da wata nasaba da ‘yan sanda.

Idan kana son ka biya lauyan da kanka:

  • A kowane lokaci kana iya ka biya kudi domin samun shawara ta fuskar shari’a
  • Cibiyar da ake neman lauyan mai karewa (DSCC) zata tuntubi lauyan ka a madadin ka.
  • Kana da ‘yancin tattaunawa a kebe ta wayar tarho tare da lauyan da ka zaba, ko kuma zai yanke shawarar zuwa ganin ka a ofishin ‘yan sanda.
  • Idan har ba’a iya tuntubar lauyan da ka zaba ba, har wa ila yau ‘yan sanda zasu iya kiran Cibiyar da ake neman Lauyan mai karewa (DSCC) domin a shirya lauyan dake aiki anan ya baka shawara ta fuskar shari’a ba tare da ka biya kudi ba.

2. Gaya wa wani kana Ofishin ‘yan sanda

  • Zaka iya gayawa ‘yan sanda su tuntubi wani wanda ya kamata ya sani cewa kana ofishin ‘yan sanda.Ba sai ka biya kudi ba.
  • Zasu tuntubi wani a madadin ka da zaran sun samu damar yin hakan.

3. Duba tsarin dokoki

  • Tsarin Dokoki wasu dokoki ne dake gaya maka abin da ‘yan sanda zasu iya yi ko kuma ba zasu iya yi ba, a yayin da kake ofishin ‘yan sanda.
  • ‘Yan sanda zasu kyale ka don ka karanta Tsarin Dokokin,amma kuma ba zaka iya daukar tsawon lokaci ba,don karantawa har ya kawo jinkiri ga ‘yansanda wajen gano cewa ko ka karya doka.
  • Idan kana son karanta Tsrain Dokokin, sai ka gayawa Jami’in ‘yan sandan dake tsare da kai.

4. Ka gaya wa yansanda idan baka da lafiya

  • Ka gayawa ‘yan sanda idan baka da lafiya ko kuma kana bukatar magani. Zasu kira likita ko nas ko kuma wasu jami’an kula da lafiya kuma ba za ka biya kudi ba.
  • Za’a iya kyale ka don ka sha maganin ka, amma sai ‘yan sanda sun duba maganin tukuna. Yawanci sai Nas ta gan ka da fari, amma kuma ‘yan sanda zasu aiko da likita idan kana bukata. Zaka iya neman ganin wani likita amma kila sai ka biya.

5. ’Yancin kin yin magana

Idan aka maka tambayoyi akan bisa kan zargin kana da hannu,ko shirya, ko haddasa aikata ta’addanci, to ba sai kayi magana ba.

Amma kuma, wannan zai iya raunata kariyar ka idan baka fadi ba a lokacin da aka tambaya ka abun, kuma daga baya a kotu ka koma ka dogara akansa.

Za’a dauki duk abinda ka fadi a mastayin shaida.

6. Samun bayani   sanin dalilin kama ka da kuma tsare ka da ake yi

  • Dole ne ‘yansanda su yi maka bayani ,domin ka gane dalilin daya sa aka kama ka, kuma aka tsare ka, kuma da zargin ka da akeyi na hannu a aikata, shirya, ko kuma haddasa aikin ta’addanci.
  • Dole ne ‘yansanda su gayawa maka dalilin da yasa suke ganin cewa dole a tsare ka a ofishin
  • Kafin a yi maka kowace irin tambaya game da zargin da ake yi maka akan hannu ko kan aikata ta’addaci, dole ne ‘yansanda sub aka da kuma lauyanka cikakken bayani kan abinda ‘yansanda ke ganin ka aikata don ka kare kanka, amma ba a lokacin da hakan zai kawo cikas ga binciken ‘yansanda ba.
  • Wannan ya shafi dukkan sauran laifukan da ‘yansanda suke zargin ka aikata.

7. Ganin rubutattun bayanai da takardu game da kama ka da kuma tsare ka da aka yi

  • Yayin da aka tsare ka a ofishin ‘yansanda, dole ne ‘yansanda su:
    • Rubuta a littafin adana bayanai tsare ka, dalilan kama ka da kuma abin da ya sa suke ganin cewa dole a tsare ka.
    • Kai da lauyanka zaku duba wadannan rubutattun bayanai. Dansandan da ke tsare da kai shi ne zai shirya wannan.
  • Dole ne ‘yansanda su baka ko lauyanka damar duba takardu da kayayyakin da za su taimaka maka wajen kalubalantar sahihancin kamunka da kuma tsare ka da aka yi.

8. Samun tafinta saboda taimaka maka da fassarorin wadansu takardu

  • Idan baka iya ko kuma baka jin turanci, to ‘yan sanda zasu shirya wani wanda ke magana da harshenka don ya taimake ka. Wannan kyauta ne.
  • Idan kuma kurma ne ko kuma kana da wata matsala wajen yin magana, ‘yan sanda zasu shirya wani mai tafinta da turanci daga masu tafinta ta hanyar nuni daga Ma’aikatar Magana ta nuni na Birtaniya don a taimakeka. Wannan kyauta ne.
  • Idan ba ka jin ko Magana da Turanci ba, ‘yan sandan za su samo maka tafinta don gaya maka dalilin da ya sa suke tsare da kai da kuma game da duk wani laifi da ake tuhumarka da aikatawa. Wannan ya zama wajibi a yi shi a duk lokacin da ‘ƴan sanda ke tsare da kai.
  • Bayan kowace shawara da aka yanke ta tsare ka kuma bayan an kama ka da wani laifi, dole ne ƴan sanda su baka wani bayani cikin harshenka na dalilin da ya sa aka tsare ka da kuma laifin da aka same ka da shi, sai dai idan akwai wasu dalilai na musamman na kasa yin haka.Waɗannan su ne:
    • Idan ka yanke shawarar ba ka buƙatar bayanin don kare kanka saboda ka fahimci abin da yake faruwa da kuma abinda zai biyo baya na rashin ƙin karɓar bayanin ka samu damar tambayar wani lauya don taimaka maka yanke shawara. Dole ne ka bayar da amincewarka a rubuce kuma.
    • Idan fassarar baki ko taƙaitawa ta hanyar wani tafinta maimakon fassara a rubuce ta wadatar maka, don ka kare kanka kuma kana da cikakkiyar fahimta game da abin da yake faruwa kuma jami’in da yake tsare da kai ya bayar da izini da wannan.
  • Idan ‘yan sanda suka yi maka tambayoyi kuma ba tare da daukar sautin maganar ba, mai yin tafinta zai rubuta wadannan tambayoyin da kuma amsoshinka a harshen da kake magana dashi. Zaka samu damar duba wannan kwafin kafin kasa hannu don tabbatar da cewa yayi daidai.
  • Idan kana son yi wa ‘yan sanda bayani, mai tafinta zai dauki kwafin wannan bayanin a harshenka domin ka duba ka ga cewa yayi daidai.
  • Haka kuma kana da hakkin samun fassarar wannan Bayani. Idan ba a sami fassara ba, ya zama dole a yi maka bayani ta hanyar tafinta sannan a samar maka da fassara ba tare da bata wani lokaci ba.

9. Mutanen da ba ‘Yan kasar Birtaniya bane

Idan kai ba dan kasar Birtaniya bane, zaka iya gayawa ‘yan sanda cewa kana san tuntubar ofishin jakadancin kasarka domin gaya musu inda kake da kuma dalilin da ya sanya kake tsare a ofishin ‘yan sanda. Za su kuma iya ziyartar ka a kebe ko kuma su aika wani Lauya don ya zo ganinka

10. Har wa ne tsawon lokaci ne za’a iya tsare ka?

  • Za a iya tsare ka har tsawon sa’o’ 48 kawai, ba tare da yi maka caji ba. Zai iya wuce haka,amma kuma sai idan wani babban jami’in ‘yan sanda ko kuma kotu ta bada umurnin a yi hakan.Kotu ta na da ikon ta zarce lokacin da aka tsare ka, ba tare da cajin ka b,a har tsawon kwana goma sha hudu, daga lokacin da aka kama ka.
  • A ko da yaushe,dole ne wani babban jami’in ‘yan sanda ya duba maganar ka don ya ga cewa ko ya kama dole a tsare ka a ofishin ‘yansanda. Ana kiran wannan sake dubawa. Ka na da ‘yancin yin magana akan wannan shawarar da aka yanke, sai fa idan baka da lafiya. Shi ma lauyan ka, yana da ikon fadin wani abu game da wannan shawarar da aka yanke a madadin ka.
  • Idan jami’i mai sake-dubawa bai sake ka ba, to dole a gaya maka abin da ya sa da kuma dalilin da aka rubuta a bayanan a lokacin da aka tsare ka.
  • Dole a sake ka idan ba wata bukatar tsare ka.
  • Yayin da ‘yansanda suka nemi kotu ta bada umarnin cigaba da tsare ka:
    • Dole ne ‘yan sanda su baka bayani a rubuce akan lokacin da kotu zata saurari karar,da kuma hujjar da ya sa aka nemi a kara tsawon lokacin da ake tsare da kai.
    • Dole ne kotu a kai ka kotu don sauraren kararka.
    • Kana da ‘yancin lauya ya kasance tare da kai a kotu.
    • Za a baiwa ‘yansanda damar tsare ka ne kawai idan kotu ta gamsu cewa hakan ya zama dole sannan da cewa ‘yansandan na cikin binciken batun ka a hankali ba tare da wani jinkiri ba.
  • Idan ‘yansanda nada isassun shaidun da za su tura ka zuwa kotu, za a iya tuhumarka a ofishin ‘yansandan ko kuma ta wasika, don ka bayyana a kotu inda don yi maka shari’a.

Sake duba da karin tsawon tsaro

  • Akwai lokuttan da za a tsare ka na har fiya da tsawone sa’o’i arba’in da takwas (48), bayan an kama ka,idan hakan ya faru, dole ne a baka wadannan abubuwan:
    • Rubutaciyyar takardan dake nuna shaidar an nemi karin tsawon lokacin da za’a tsare ka;
    • Lokacin da aka ne mi karin tsawon lokacin;
    • Lokacin da kotu zata saurari bayanin neman karin tsawon lokacin
    • Dalilan da suka sa aka nemi karin lokacin tsareka.

Dole ne a baka bayabai ( ko lauyan ka) duk lokacin da aka nemi karin tsawon lokacin tsare ka.

11. Damar ganin shaidu idan shari’arka ta je kotu

Idan aka tuhume ka da wani laifi, dole a baka ko lauyanka damar ganin shaidar samin ka da laifi da kuma shaidun da za su iya taimaka maka wajen kare kanka. Dole ne a yi wannan kafin a fara shari’arka. ‘Yansanda da kuma Hukumar Gabatar da kararraki ta Ingila ne ke da alhakin shirya wannan da kuma samar da damar ganin takardu da kayayyakin da suka jibanci tuhumar.

Wasu abubuwan da ya kamata ka sani kan zama cikin ofishin ‘Yan sanda

Yadda ya kamata a kula da kai da kuma dawainiyarka

Wadannan takaittun bayanai ne akan abin da ya kamata ka yi la’akari dasu yayin da kake ofishin ‘yan sanda. Idan kana son Karin bayani,sai ka nemi ganin Tsarin Dokoki. Sun kunshi jerin sunayen inda zaka samo karin bayanai akan wadannan abubuwa. Ka tambayi Jami’in ‘yan sanda dake tsare da kai idan kana da wasu tambayoyi.

Mutanen dake Bukatar Taimako

  • Idan shekarun ka basu wuce goma sha takwas ba (18) ko kana da matsalar kaifin kwakwalwa, misali tabin hankali ,to dole ne ka samu wani ya kasance tare da kai a lokacin da yan’sandan ke yin wasu abubuwa. Ana kiran wannan “mutumin da ya cancanta”, kuma za’ a ba su kwafi na wannan bayani.
  • Dole ne wannan mutumin da ya cancanta ya kasance yana tare da kai a lokacin da ‘yan sanda suke fada maka ‘yancin ka da kuma dalilin da ya sanya aka tsare ka a ofishin ‘yan sanda. Dole shi ko kuma ita su kasance tare da kai a lokacin da ‘yan sanda ke karanta maka gargadin.
  • Mutumin da ya cancanta zai kuma iya neman Lauya a madadinka .
  • Zaka iya tambayar Lauyanka ba tare da mutumin da ya cancanta a dakin ba, idan kana son yin hakan.
  • Kuma kila ‘yan sanda su bukaci yin daya daga cikin abubuwan da aka lissafa a kasa yayin da kake ofishin ‘yan sandan. Dole mutumin da ya cancanta, ya kasance yana tare da kai a duk tsawon lokaci, sai dai kuma idan akwai dalilai na musamman, idan ‘yan sanda suka yi kowane abu daga cikin wadannan abubuwan:
    • Su dauki hoto ko yi maka tambayoyi ko kuma neman ka don ka sa hannu a wani jawabin da aka rubuta ko kuma bayanan ‘yan sanda.
    • Cire tufafin ka domin a bincike ka.
    • Daukar hoton yatsunka, hoto ko daukar kwayar hallita watau DNA ko kuma wani gwajin.
    • Ka shiga layin jerin mutane da ake yi da nufin samun shaida.
  • Dole a baiwa mutumin da ya cancanta ganinka ko kuma yin magana ta waya, a lokacin da ‘yan sanda ke sake duba batun ka, don su ga cewa ko akwai hujjar ci gaba da tsare ka.
  • Idan mutumin da ya cancanta na nan, dole ne ya kasance a wurin a lokacin da ‘yansanda suka caje ka da laifi.

Samun bayanai a lokacin da kake cikin ofishin ‘yan sanda

  • An ajiye duk bayanan abinda ya same ka a lokacin da ka ke cikin ofishin ‘yan sanda. Ana kiranshi Bayanan da aka rubuta a lokacin da kake tsare.
  • Idan ka bar ofishin ‘yan sanda,kai ko Lauyan ka ,ko mutumin da ya cancanta zai iya neman a bashi kwafi na wannan bayanan da aka rubuta a lokacin da kake tsare. Dole ne ‘yan sanda su baka kwafi na bayanan da aka rubuta a lokacin da kake tsare ba da wani bata lokaci ba.
  • Zaka iya tambayar ‘yan sanda su baka bayanan da aka rubuto a lokacin da kake tsare har tsawon watanni goma sha biyu bayan ka bar ofishin ‘yan sandan

Sanar da wani

  • Bayan kayi magana da Lauya da kuma sanar da wani cewa an tsare ka, za’a iya barinka, kayi amfani da wayar tarho sai daya.
  • Ka tambayi ‘yan sanda idan kana son ka yi waya.
  • Kuma zaka nemi a baka alkalami da takarda.
  • Za’a kuma iya ziyartar ka amma kuma Jami’in dake tsare da kai zai iya hana yin hakan.

Dakin da ake tsare da kai

  • Idan da hali, ya kamata a ajiye ka a dakin kurkuku kai kadai.
  • Dole ne ya kasance da tsabta, da dumi da kuma haske.
  • Dole ne zannuwan gadonka su kasance cikin tsabta kuma a gyare.
  • Dole ne a kyale ka yin amfani da bayangida sannan kuma baka damar yin wanka.

Tufafi

Idan an karbe tufafin ka, to dole ne ‘yan sanda su baka wasu tufafi.

Abinci da Sha

Dole a baka abinci sau 3 a rana tare da abin sha. Kuma zaka iya samun abin sha a tsakanin lokuttan da ake baka abinci.

Motsa jiki

Idan ya yiwu, dole ne a kyale ka, ka fita waje a kowace rana don shan iska.

Idan ‘yan sanda sun tambayeka

  • Dole dakin ya zama da tsabta,da dumi da kuma haske.
  • Ba dole bane ka tashi tsaye.
  • Dole Jami’an ‘yan sanda su gaya maka sunayensu da mukaminsu.
  • Dole ne a bar ka samun walwala a lokuttan cin abinci da kuma baka damar shan ruwa bayan kimanin sa’o’i biyu.
  • Akalla dole a kyale ka, ka huta har tsawon sa’o’i 8 a cikin sa’o’i 24 da ake tsare da kai.

Bukatun Addini

Gaya wa ‘yansanda idan kana bukatar kowane irin abu da zai taimaka maka gudanar da addininka yayin da ka ke cikin ofishin. Za su iya samar da littattafan addini da sauran abubuwa, idan da bukatar hakan.

Lokuttan da dokokin da aka sani suka banbanta

Samun Lauya don ya taimakeka

Akwai wasu lokutta da ya kamata ‘yan sanda su yi maka tambayoyi da gaggawa kafin kayi magana da Lauya. An bada bayanan wadannan lokuttan na musamman a Tsarin Dokoki. Wannan littafi ya tsara abubuwan da ‘yan sanda zasu yi ko kuma ba zasu iya yi ba, yayin da kake tsare a ofishin ‘yan sanda. Idan kana son ka duba bayani,suna cikin sakin layin na 6.7 na tsarin na dokoki na H na Tsarin Dokoki.

Akwai wani lokaci na musamman da ‘yan sanda ba zasu kyale ka, yin magana da Lauyan da ka zaba ba. Idan haka ya faru, to dole ne a kyale ka don ka zabi wani Lauya. Idan kana son duba bayanai, yan cikin jerin bayanai a jerin B na Code H na tsarin Dokoki.

Akwai wani lokacin da ‘yan sanda ba za su kyale ka ka yin Magana da lauyan ka ba. Wannan lokaci ne da babban jami’in ‘yansanda ya bada izini wa sufeto dake cikin kayan ya kasance anan. Zaka iya duba sakin layi na shida da rabi (6.5) na H na tsarin dokokin, domin samun cikkaken bayani.

Gayawa wani cewa kana Ofishin ‘yan sanda

Akwai wasu lokutta da ‘yan anda ba za su kyale ka tuntubar kowa ba. An bada bayanan wadannan lokutta a Tsarin Dokokin. Idan kana son duba bayanai, a jerin bayanai suna jerin B na tsarin dokokin H na tsarin Dokoki.

Masu ziyara dake zaman kansu

Akwai wasu a kungiyar jama’a da ake barin su tafi ofisoshin ‘yan sanada bada wata sanarwa ba. Ana kiransu masu zaman kansu dake ziyarar kurkuku kuma suna aiki ne ba tare da biyansu ba domin tabbatar da cewa ana kula da mutanen da ke tsare kuma suna da ikon samun abubuwan da yake ‘yancinsu ne.

Ba ka da damar ganin masu ziyarar dake zaman kansa, ko kuma ka nemi su ziyarce ka, amma mai ziyarar zai iya neman saduwa sa kai.Idan wani mai ziyara dake zaman kanshi ya ziyarce ka yayin da kake daure, zai duba ko an kare lafiya da kuma ‘yancinka,ba tare da hannun ‘yan sanda ba. Amma kuma ba dole bane ka yi magana dasu idan baka bukata.

Yadda zaka kai kara

Idan kana son ka kai kara kan yadda ake kulawa da kai, sai ka nemi ganin jami’in ‘yansanda wanda yake sufeto ne ko kuma wani babban jami’i. Bayan an sake ka, zaka iya kai kara a duk wani ofishin ‘yan sanda, ko Hukumar gabatar da kara ta ‘yansanda mai zaman kanta (IOCC) ko wurin Lauyan ka ko kuma dan Majlisar dokoki a madadin ka.